Romans 12

Hadayu Masu Rai

1Saboda haka, ina roƙonku, ʼyanʼuwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah-wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya. 2Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake-abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.

3Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku: Kada yǎ ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari yǎ auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa. 4Kamar dai yadda kowannenmu yake da jiki ɗaya da gaɓoɓi da yawa, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba, 5haka ma a cikin Kiristi mu da muke da yawa mun zama jiki ɗaya, kuma kowace gaɓar ɗanʼuwan sauran ne. 6Muna da baye-baye dabam dabam, gwargwadon alherin da aka yi mana. In baiwar mutum ta yin annabci ce, sai yǎ yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarsa. 7In ta hidima ce; sai yǎ yi hidima. In kuma ta koyarwa ce, sai yǎ koyar; 8in ta ƙarfafawa ce, sai yǎ ƙarfafa; in kuma ta ba da taimako ce don biyan bukatun waɗansu, sai yǎ yi haka hannu sake; in ta shugabanci ce, sai yǎ yi shugabanci da himma; in ta nuna jinƙai ce, sai yǎ yi haka da faraʼa.

Ƙauna

9Dole ƙauna ta zama ta gaskiya. Ku ƙi duk abin da yake mugu; ku manne wa abin da yake nagari. 10A game da ƙaunar ʼyanʼuwa kuwa, ku ƙaunaci juna gaya. A wajen ba da girma, kowa yǎ yi ƙoƙari wajen girmama wani fiye da kansa. 11Kada ku zama marasa himma, sai dai masu himma a ruhaniyarku, kuna bauta wa Ubangiji. 12Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin adduʼa. 13Ku taimaki mutanen Allah masu bukata. Ku zama masu karɓan baƙi.

14Ku sa wa masu tsananta muku albarka; ku sa albarka kada fa ku laʼanta. 15Ku yi murna da masu murna, ku yi kuka da masu kuka. 16Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna girmankai, sai ma ku riƙa cuɗanya da talakawa. Kada ku zama masu ɗaga kai.

17Idan kowa ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta. Ku lura don ku aikata abin da kowa zai iya gani cewa daidai ne. 18Ku yi iya ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa. 19Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa: “Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka,”
M Sh 32.35
in ji Ubangiji.
20A maimakon haka:

“In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ciyar da shi;
in yana jin ƙishirwa, ka ba shi ruwan sha.
Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta a kansa.”
K Mag 25.21, 22

21Kada ku bar mugunta ta sha kanku, sai dai ku sha kan mugunta ta wurin aikata nagarta.

Copyright information for HauSRK